Iran: Kungiyar Bada Agajin Gaggawa Ta Kasar Iran Ta Kawo Karshen Ayyukanta A Kasar Lebanon

2020-08-22 11:46:57
Iran: Kungiyar Bada Agajin Gaggawa Ta Kasar Iran Ta Kawo Karshen Ayyukanta A Kasar Lebanon

Kungiyar bada agajin gaggawam ko Hilar Ahmar ta kasar Iran ta bada sanarwan cewa ta kawo karshen ayyukanta a birnin Beirut na kasar Lebanon bayan jinyan mutane kimanu 3,500.

Majiyar muryar Jumhuriyar Mususlunci Iran ta nakalto Muhammad Baqir Muhammadi shugaban tawagar Hilal Ahmar ta kasar Iran a birnin Beirut ya na cewa a cikin kwanaki 17 da kafa asibitin wucin gadi a birnin sun gudanar da ayyukan jinya da dama wadanda suka hada da tiyata mai sauki da kuma masu nauyin.

Labarin ya kara da cewa bayan fashe-fashen da suka faru a ranar 4 ga watan Augustan da muke ciki ne, wanda kuma ya kashe mutane kimani 170 sannan wasu kimani 7000 suka ji rauni, gwamnatin Iran ta kafa asibitin wucin gadi a birnin na Beirut don taimakawa wadanda suka ji rauni sanadiyyar fashewar.

Banda wannan Iran ta aike da ton 95 na magunguna da kuma kayakin abinci zuwa kasar ta Lebanon bayan fashewar.

Tags:
Comments(0)