Kungiyar ECOWAS Zata Aike Da Tawaga Zuwa Mali Don Maidawa Kaita Shugabancin Kasar

2020-08-22 11:39:46
Kungiyar ECOWAS Zata Aike Da Tawaga Zuwa Mali Don Maidawa Kaita Shugabancin Kasar

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS za ta aike da tawaga zuwa kasar Mali a wani kokari na kawo karshen juyin mulkin da sojoji suka yi wa Bubakar Kaita.

Kamfanin dillancin laraban reuters ya nakalto shugaban kungiyar na karba-karba, kuma shugaban kasar Niger Muhammad Yusuf ya na fadar haka a ranar Alhamis bayan wata tattaunawa tsakanin shuwagabannin kungiyar.

Yusuf ya bayyana cewa kungiyar za ta aika da tawagar shugabannin kasashe 4 tare da jagorancin tsohon shugaban kasar Najeriya Mr Goodluck Jornathan, don ganin an maida Kaita kan kujerar shugabancin kasar.

Sai dai majiyar kungiyoyin yan adawa a kasar suna cwae ba za su taba amincewa Kaita ya dawo kan kujerar shugabncin kasar ba.

Har’ila yau ‘yan adawan sun bukaci kasashen waje su daina shishigi a cikin harkokin cikin gida na Kasar.

A ranar tarlatan da ta gabat ce sojoji suka kwace mulki a kasar ta Mali bayan tashe-tashen hankula na makonni a kasar.

Tags:
Comments(0)