Iran:Ragowar Iraniyawa Wadanda Aka Yi Garkuwa Da Su A Somalia Sun Dawo Gida

2020-08-22 11:09:21
Iran:Ragowar Iraniyawa Wadanda Aka Yi Garkuwa Da Su A Somalia Sun Dawo Gida

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bada sanarwan cewa mutane uku masu kamun kifa ko su wadanda barayi na kan ruwa na kasar Somalia suka yi garkuwa da su sun dawo gida.

Majiyarmuryar muryar Jumhuriyar Musulunci ta Iran (MJI) ta nakalto Waliyullahi Muhammadi jami’ii mai kula da lamuran kasashen Afirka a ma’aikatar harokin waje kasar ya na fadar haka a ranar Alhamis.

Muhammadi ya kara da cewa a shekara ta 2015 ne ‘yan fashi a doron ruwa na kasar Somaliya suka yi garkuwa da Iraniyawa 37 masu aikin kamun kifa ko su a tekun Somalia inda suka bukaci a basu kudaden fansa kafin sakin su.

Amma ma’aikatar harkokin wajen ta bayyana cewa tawagogi guda biyu na wadanda aka yi garkuwan da su sun sami damar tserewa daga hannun yan fashin kuma sun dawo gida.

Labarin ya kara da cewa mutane uku da suka raje sun sami damar kubuta daga hannun barayi na kan ruwan ne a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata.

Muhammadi ya yabawa wasu kungiyoyin sa kai da kuma kare na hakkin bil’adama wadanda suka taimaka wajen ganin an kubutar da Iraniyawan daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su.

Tags:
Comments(0)