Iran: Amurka Ba Za Ta Kai Ga Manufofinta Na Baya –Bayan Nan A MDD Ba

2020-08-22 10:53:43
Iran: Amurka Ba Za Ta Kai Ga Manufofinta Na Baya –Bayan Nan A MDD Ba

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa gwamnatin kasar Amurka ba za ta kai ga mummunan manufofinta kan kasar Iran a kwamitin tsaro na MDD ba.

Majiyar muryar jumhuriyar Musulunci ta Iran (JMI) ta nakalto Sa’id Khatib Zade kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran yana fadar haka a jiya Jumma’a . Ya kuma kara da cewa gwamnatin kasar Amurka ta na son ta yi amfani da wata ka’ida a cikin yarjejeniyar shirin Nukliyar kasar Iran ta JCPOA don maida takunkuman tattalin arziki na MDD kan kasar.

Khatib zade ya kara da cewa ganin cewa gwamnatin kasar Amurka ta rika ta bayyana ficewarta daga cikin yarejejeniyar tun cikin watan Mayun shekara ta 2018, sannan sauran kasashe da suka ci gaba da goyon bayan yarjejeniyar sun ci gaba da harkokinsu ba tare da Amurka ba, yanzun kuma Amurka ba ta da hurumin amfani da wani bangare na yarjejeniyar don cimma wasu manufofinta ba.

Labarin ya kara da cewa wadannan kasashe tuni sun yi watsi da bukatar da Amurka ta gabatarwa kwamitin tsaro na MDD da wannan manufar.

Tags:
Comments(0)