Dubban Falasdinawa Sun Halarci Sallar Jumma’a A Masallacin Al-Aqsa

2020-08-22 10:47:24
Dubban Falasdinawa Sun Halarci Sallar Jumma’a A Masallacin Al-Aqsa

Dubban Falasdinawa sun sami halattar sallar jumma’a a jiya a masallacin Al-aqsa duk tare da hanawa da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila (HKI) suka yi suke yi.

Wata majiyar labarai ta yanar gizo ta kuma Falasdinawa ta bayyana cewa akalla falasdianwa dubu 10 ne suka sami damar halattar sallar jumma’a a iya a masallacin, duk da cewa jami’an tsaron yahudawan Isra’ila suna son hana halattar sallar.

Sheikh Yusuf Abu Saninah limamin da ya jagorancin sallar jumma’a a birnin Qudus ya bukaci falasdinawan da su yawaita sallah a masallacin don hana yahudawan cimma burinsu na kwace masallacin.

Labarin ya kara da cewa a sauran sassan kasar Falasdinu da aka mamaye kuma, falasdinawan sun fito zanga-zangar yin allawadai da yahudawan, wadanda suke ci gaba da kwace filaye da rusa gidajen Falasdinawa a yankuna daban –daban.

Har ila yau, jiya ce 21 ga watan Augusta, ake cika shekaru 51 da kona masallacin al-aqsa wanda wani bayahude sahyoniyya ya yi a shekara 1969.

Tags:
Comments(0)