Kungiyoyin Gwagwarmaya A Kasar Iraki Sun Sha Alwashin Tsananta Kai Wa Sojojin Mamayar Amurka Hare-hare Matukar Ba Ta Fice Daga Kasar Ba Cikin Ruwan Sanyi

2020-08-21 15:57:29
    Kungiyoyin Gwagwarmaya A Kasar Iraki Sun Sha Alwashin Tsananta Kai Wa  Sojojin Mamayar Amurka Hare-hare Matukar Ba Ta Fice Daga Kasar Ba Cikin Ruwan Sanyi

A wani bayani da su ka fitar bayan ziyarar da Fira ministan kasar Mustafa Kazimi ya kai Amurka, kungiyoyin gwagwarmayar ta kasar Iraki sun ce; Mu tsammaci cewa idan ya je zai zama mai wakiltar IRaki da al’ummarta domin tabbatar da cin gashin kan kasa, ba wai ya zama mai sauraron shifta daga wawan shugaban kasar Amurka da ya kware waje sace dukiyoyin al’ummu ba da zubar da jininsu.

Bayanin kungiyoyin gwagwarmayar ya ci gaba da cewa; Abinda Kazimi ya kamata ya bai wa muhimmanci shi ne aiwatar da kudurin al’ummar Iraki da miliyoyinsu su ke gudanar da Zanga-zanga akai, wato kawo karshen mamayar da Amurka ta yi wa Iraki.

Wani sashe na bayanin ya ci gaba da cewa; Bayan ta’annatin da Amurka ta yi wa kasar Iraki, mun yi mamakin yadda a yayin ziyarar tashi zuwa Washington, Fira minstan bai yi Magana akan batun ficewar sojojin Amurka daga Iraki ba.

Har ila yau, kungiyoyin gwagwarmayar Iraki sun ce; ta fuskar doka suna da hakkin tsananta kai hare-hare akan duk wani abu mai amfani na Amurka dake cikin Iraki, matukar ba su fice daga cikin wannan kasa ta ruwan sanyi ba.

Tags:
Comments(0)