Amir Jafari

An haifi Jafari, Amir a ranar daya ga watan Satumba shekarar Alif dari tara da saba'in da hudu a birnin Tehran. Jafari ya yi karatunsa a fannin nazarin Kula da Ayyuka a Jami'ar Musulunci na Azad kuma ya ci gaba da yin karatu a fannin wasan kwaikwayo a Cibiyar Samandarian.

Ya fara futowa a wasansa na farko a shekara ta dubu biyu da daya a fim mai suna ‘Bread, Love and 1000cc Bike’. An hasko shi a jerin wasa mai suna ‘No Words Needed’, wanda Mehdi Mazloumi ya shirya a wannan shekarar.

Jafari ya bayanna a cikin fina-finai da dama da suka hada da ‘Poisonous Mushroom’ (a shekarar ta dubu biyu da daya), ‘Down and Out’ (a shekarar ta dubu biyu da bakwai), ‘The Postman Doesn't Ring Three Times’ (a shekarar ta dubu biyu da takwas), ‘The Snitch’ (a shekarar ta dubu biyu da tara), ‘The Pickpocket of the South Street’ (a shekarar ta dubu biyu da goma), ‘Thirteen’ (a shekarar ta dubu biyu da goma sha biyu), ‘The Rules of Accidents’ (a shekarar ta dubu biyu da goma sha biyu), ‘Block 9, Exit 2’ (a shekarar ta dubu biyu da goma sha uku), ‘Stranger’ (a shekarar ta dubu biyu da goma sha uku) da ‘Confession of My Dangerous Mind’ (a shekarar ta dubu biyu da goma sha hudu).

Wasu daga cikin jerin wasannin da ya futo su ne ‘I’m a Tenant’ (a shekarar ta dubu biyu da uku), ‘The Forbidden Fruit’ (a shekarar ta dubu biyu da bakwai), ‘Privacy Policy’ (a shekarar ta dubu biyu da tara), ‘Under the Vestibule’ (a shekarar ta dubu biyu da goma), ‘The Bounced Check’ (a shekarar ta dubu biyu da goma sha daya) da kuma ‘Madness of Love’ (a shekarar ta dubu biyu da goma sha daya).

1
Share

Fina-finai da Jerin fina-finai

The Bounced Check

The Bounced Check