Afsaneh Bayegan

An haifi Bayegan, Afsaneh a shekara ta Alif dari tara da sittin da daya a birnin Tehran.

Afsaneh Bayegan ta fara sana'ar ta ne na zama 'yar wasan kwaikwayo a shekara Alif dari tara da saba'in da biyu a wani gajeren wasa mai suna ‘Horn’ wanda Ali Alizadeh ne ya shirya.

A shekarar Alif dari tara da tamanin da hudu da ta kware a sana'ar, sai aka saka ta a cikin jerin wasa mai tsayi mai suna ‘Sarbedaran’.

Fim dinta na farko a yayin da ta zama babba shi ne ‘Missing’ (a shekara ta Alif dari tara da tamanin da biyar). Daga bisani ta bayyana a wasu nau'o'i wasanni kuma ta zama daya daga cikin jaruman 'yan wasa na Iran a shekarun Alif dari tara da tamanin har izuwa shekarun Alif dari tara da casa'in.

Wasu daga cikin fina-finan da ta bayyana sun hada da ‘Maryam and Mitil’ (a shekara ta Alif dari tara da casa'in da uku), ‘Strange Sisters’ (a shekara ta Alif dari tara da casa'in da biyar), ‘The Wrong Guy’ (a shekara ta Alif dari tara da casa'in da bakwai), ‘Kanan’ ( a shekara ta dubu biyu da bakwai) da kuma ‘Superstar’ (a shekara ta dubu biyu da takwas).

Ta kuma taka rawar gani a jerin wasannin talabijan da yawa, ciki har da ‘Day of Envy’ (a shekara ta dubu biyu da takwas) da kuma ‘Code White’ (a shekara ta dubu biyu da takwas).

Saboda matsayinta a wasa mai suna ‘Strange Sisters’ (a shekara ta Alif dari tara da casa'in da biyar) ta samu babban lamban yabon diploma na fitaccen Jaruma a bikin baja kolin fina-finan duniya na Fajr a karo na goma sha hudu.

1
Share

Fina-finai da Jerin fina-finai

The Wrong Guy

The Wrong Guy