Alireza Kamali-Nejad

Alireza Kamali - Nejad (Haifaffan shekarar 1980 ne, a Tehran).

Kamali-Nejad ya yi karatun Zane-zane a Jami'ar Tehran, inda ya shiga cikin wasan kwaikwayon mutum mutumi (Puppet shows). A shekara ta 2003, ya karbi mukamin mataimakin darektan jerin shirin siris 'Sheikh Baha'ee' (2002). Bayyanar sa ta farko a TV ta kasance a cikin jerin jerin siris wanda akai akan Ashura, wadda ba a kammala ba, kuma ba a saki fim din ba. Ya jawo hankalin jama'a bayan da ya yi fim din 'The Kingdom of Solomon' (2010). Daga cikin sauran fina-finai sa akwai 'Travel' (2003), 'The End of the Road' (2007), 'Empty Hands' (2005), 'The Outcasts' (2006), da kuma 'This is another City' (2011). Ya kuma bayyana a jerin fim sdin siris da yawa, ciki har da 'Life Again' (2004), 'A Stairway to Heaven' (2007), 'The Decius City' (2008), 'Heart of Ice' (2011), da kuma 'A Beautiful Revolution' (2014).
1
Share

Fina-finai da Jerin fina-finai

The Kingdom of Solomon the Prophet

The Kingdom of Solomon the Prophet