Ali Mosaffa

Musaffa, Ali (an haife shi a 1 ga watan disambar 1966, Tehran)

Dan wasa kuma mai bada umurni Ali musaffa ya kammala katun injiniyan gine-gine (Civil Engineering) a jami’ar Tehran a 1995.

Shirin farko da ya taka rawa a cikinsa shine fim din ‘Hope’ (1991).

Yayi kaurin sunane bayan taka rawar da yayi a cikin fim din ‘Pari’ (1995) da kuma ‘Leila’ (1997).

Yana da Karin kwarewa a shirin tarihi (documentary), gajerun (short), mai bada umurni kuma marubuci.

Musaffa ya samu kyaututtuka da dama ciki har da FIPRESCI Prize, da Karlovy Vary na International Film Festival, akan aikin bada umurni da yayi na fim din ‘The Last Step’ (2012), sannan ya samu kyautar  crystal simorgh na Fajr International Film Festival akan zubin fim din a matsayin tauraro.

Bugu da kari ya samu difilomar girmamawa daga Fajr International Film Festival akan rawar da ya taka a fim din ‘Beloved Sky’ (2011), da kuma kyautar Crystal Simorgh daga Fajr International Film Festival akan rawar da ya taka a fim din ‘Pari’ (1995).

1
Share

Fina-finai da Jerin fina-finai

The British Briefcase

The British Briefcase