Abdorreza Akbari

Akbari Abdurridha ( Haihuwar Tehran, 14 ga watan Farbardin, 1332 hijira shamshiyya)

Tun a 1347 ne, Abdurridha, ya fara cikin fagen cibiyoyin samari da matasa, inda ta fara yin wasannin kwaikwayo na dandali.

Tare da abokansa samari su ka kafa kungiyar wasannin kwaikwayo na dandali na garin Najaf Abad, suka kuma kasance a karkashin sanya idanu da kulawar masana kamar Daryush Muaddabiyan, da Behzan Farahani, da su ka rika ba su horo.

A cikin shekarar 1363 ne wannan dan wasan, ya taka rawa a cikin fim din ( Zindani Dole Tu) wanda aka nuna a silima.

Akbari, ya kuma kasance a cikin fina-finai irinsu ( Pahaban Namemirad) 1376,  ( Tawallud Dige) 1377, ( Igma) 1386, ( Amaliyyat 125), 1387, ( Dilnabazan) 1388 ( Shauq Farbaz) 1390.

Abdorreza
Share