Behnam Tashakkor

An haifi Tashakkor, Behnam a ranar ashirin da hudu ga watan Janairu shekara ta Alif dari tara da saba'in da bakwai a garin Bandar-e Anzali.

Behnam Tashakkor ya sami digiri dinsa na farko a tattalin arziki na Harkokin Kasuwanci daga Jami'ar Nazraz Kooh Islamic Azad.

Shirin farkon sa ya fara ne a shekarar Alif dari tara da casa'in da shida a garin Sari na kasar Iran. Ya kuma yi aiki a fannin nade-naden fina-finai har shekara biyu.

A shekara ta dubu biyu da takwas , ya yi aiki a fannin gabatar da shirye-shirye a rediyo.  A shekarar dubu biyu da tara Tashakkor ya zama cikakken Jarumin kwaikwayo.

Ya bayyana a cikin wasan kwaikwayon ‘The Scarlet Pearl’ (a shekara ta dubu biyu da hudu zuwa biyar), ‘Made in Iran’ (a shekara ta dubu biyu da goma sha daya zuwa sha biyu), ‘Cops and Robbers’ (a shekara ta dubu biyu da goma sha biyu) and ‘Chimney’ (a shekara ta dubu biyu da goma sha uku).

Ya kuma futo a fina-finai irin su: ‘Resurrection Day’ (‘Hussein Who Said No’) (a shekara ta dubu biyu da goma) and ‘Reparation’ (a shekara ta dubu biyu da goma sha daya).

Ba Iranen ya futo a matsayin mai magana a cikin wasan kwaikwayon ‘Pejman’ a shekara ta dubu biyu da goma sha uku.

Ya zama sananne ne bayan ya futo a matsayin Dr. Nima a cikin jerin wasannin ‘Medical Building’ (a shekara ta dubu biyu da goma zuwa sha daya).

1
Share