Behnoush Bakhtiyari

An haifi Bakhtiyari, Behnoush a ranar goma sha tara ga watan Mayu shekara ta Alif dari tara da saba'in da biyar a birnin Tehran. Behnoush Bakhtiyari ta yi karatun ta  a fannin nazarin harshen Faransanci a Jami'ar Azad Jami'ar Iran. Ta kara yin karatun shekara daya a fannin wasan kwaikwayo a makarantar Rassam Honar. 

Ta fara aiki a matsayin ta na mai kula da rubuce-rubucen wasanni kafin ta zama Jaruman kwaikwayo. Behnoush Bakhtiyari  ta fara futowa ne a wasan  'Fresh Air' (a shekara ta Alif dari tara da casa'in da shida), wanda Mohammad Rahmanian ya shirya.

Bakhtiyari ta bayyana a fina-finai masu yawa ciki har da su  ‘Checkmate’ (a shekara ta dubu biyu da bakwai), ‘Ten Figures’ (a shekara ta dubu biyu da takwas), ‘The Outcasts 3’ (a shekara ta dubu biyu da goma), ‘Hectic Times’ (a shekara ta dubu biyu da goma sha daya), 'The Carriage' (a shekara ta dubu biyu da goma sha uku) da ‘Men are not angels’ (a shekara ta dubu biyu da goma sha hudu).

Ta kara bayyana a jerin shirye-shiryen talabijin irin su ‘Homeless’ (a shekara ta dubu biyu da hudu), ‘The Nights of Barareh’ (a shekara ta dubu biyu da biyar), ‘Checkered’ (a shekara ta dubu biyu da bakwai), ‘The Rich and the Poor’ (a shekara ta dubu biyu da tara), ‘Goodbye Child’ (a shekara ta dubu biyu da goma sha biyu), ‘Detour’ (a shekara ta dubu biyu da goma sha biyu), ‘The Good, the Bad and the Ugly’ (a shekara ta dubu biyu da goma sha hudu) da kuma ‘Flower and Nightingale Neighborhood’ (a shekara ta dubu biyu da goma sha biyar).

A shekara ta dubu biyu da goma sha biyar, an zabe ta don kyautar  lambar yabon jarimar Jaruma domin matsayin ta a wasa mai suna 'I' na Fajr International Film Festival, sashi na talatin da hudu.

1
Share