Babak Hamidiyan

An haifi Hamidiyan, Babak a ranar goma ga watan Satumba a shekarar Alif dari tara da tamanin. Hamidiyan ya yi karatu ne a fannin wasan kwaikwayo daga Jami'ar Azad ta Musulunci. Ya fara sana'arsa na wasan kwaikwayo a kan dandamali. Bayan ya hadu da wani dan wasa mai suna Atila Pesyani, ya shiga kungiyar 'yan wasan kwaikwayo mai suna 'Bazi group'.

Wasansa na farko da aka hasko shi  shi ne ‘My Father's Farm’ (a shekarar dubu biyu da uku).

Ya kara bayyana a fina-finai irin su ‘Qadamgah’ (a shekarar dubu biyu da uku), ‘Big Drum Under the Left Foot’ (a shekarar dubu biyu da hudu), ‘A Little Kiss’ (a shekarar dubu biyu da biyar), ‘God is Near’ (a shekarar dubu biyu da shida), ‘Down-and-Out’ (a shekarar dubu biyu da bakwai) da kuma ‘Resurrection Day’ (‘Hussein Who Said No’) (a shekarar dubu biyu da goma).

An zabi Hamidiyan domin bada lambar yabon bikin baja kolin Silimar Iran na Gwarzon Jarimi domin matsayinsa a wasa mai suna ‘Big Drum under the Left Foot’ (a shekarar dubu biyu da hudu). Ya ci kyautar lambar yabo a bikin baja kolin Silimar Iran na Gwarzon Jarimi domin matsayinsa a wasa mai suna  ‘The Wrangler’ (a shekarar dubu biyu da bakwai).

Babbar rawar da ya taka a fina-finan ‘The Resurrection Day’ (‘Hussein Who Said No’) (a shekara ta dubu biyu da goma) da ‘Ch (Chamran)’ (a shekara ta dubu biyu da goma sha uku) ya sa ya samu nasara sosai har da cin kyautar lambar yabon Crystal Simorghs na Gwarzon Jarimi a bikin baja kolin fina-finai ta duniya na Fajr.

Ya kara samun lambar yabon Gwarzon Jarimi daga Iranian Cinema Critics Association Award saboda matsayinsa a wasa mai suna ‘Hush! Girls Don't Scream’ (a shekara ta dubu biyu da goma sha uku).

1
Share

Fina-finai da Jerin fina-finai

Hallucinations

Hallucinations