Azita Hajiyan

An haifi Hajiyan, Azita a ranar goma sha daya ga watan Janairu a shekara ta Alif dari tara da hamsin da takwas a garin Tehran.

Hajiyan tana da digiri din ta a fannen wasa da bada umarni kuma ta fara sana'ar a shekara ta Alif dari tara da saba'in da biyar inda ta futo a wasa mai suna ‘Shine on, Lady Sunshine’. Wasan ta na farko shi ne ‘Doll Thief’ wanda Mohammad Reza Honarmand ya shirya a shekara ta Alif dari tara da tamanin da tara.

Ta bayyana a fina-finai da dama kamar irin su ‘The Magical Journey’ (a shekara ta Alif dari tara da casa'in),  ‘Actor’ (a shekara ta Alif dari tara da casa'in da biyu), ‘Snowman’ (a shekara ta Alif dari tara da casa'in da hudu), ‘Cloud and Sun’ (a shekara ta Alif dari tara da casa'in da shida), ‘Red Ribbon’ (a shekara ta Alif dari tara da casa'in da takwas), ‘The Equation’ (a shekara ta dubu biyu da uku), ‘Candle in the Wind’ (a shekara ta dubu biyu da uku), ‘Mahya’ (a shekara ta dubu biyu da bakwai), ‘The Wall’ (a shekara ta dubu biyu da bakwai), ‘Gold and Earth’ (a shekara ta dubu biyu da takwas) da ‘The Orange Taxi’ (a shekara ta dubu biyu da takwas).

Daga cikin jerin wasanni masu tsayi data bayyana, akwai su  ‘Imam Ali’ (a shekara ta Alif dari tara da casa'in da bakwai), ‘Khazra High School’ (a shekara ta Alif dari tara da casa'in da bakwai), ‘The Green Journey’ (a shekara ta dubu biyu da daya), ‘Unbreakable Mirrors’ (a shekara ta dubu biyu da takwas), ‘Until Being with Sorayya’ (a shekara ta dubu biyu da daya) da kuma ‘Kimiya’ (a shekara ta dubu biyu da goma sha biyar).

Domin matsayinta a wasa mai suna ‘Red Ribbon’ (a shekara ta Alif dari tara da casa'in da takwas), taci lambar yabon fitacciyar jarimar a bikin bajakolin fina-finan duniya na Crystal Simorgh na Fajr.

Tsohon mijin Hajiyan shima Jarumin Iran ne mai suna Mohammad Reza Sharifinia. 'Ya'yansu biyu, Mehraveh da Melika Sharifinia, suma su na wasan kwaikwayo.

1
Share

Fina-finai da Jerin fina-finai

Imam Ali

Imam Ali