Abbas Amiri-Moqaddam

An haifi Amiri-Moqaddam, Abbas a shekarar Alif dari tara da hamsin a garin Amol kuma ya mutu a ranar ashirin da shida ga watan Fabrairun dubu biyu da goma sha daya a garin Rasht.

Bayan kammala karatun sakandare, Abbas Amiri-Moqaddam ya shiga kungiyar 'yan wasa a birnin Rasht inda ya fara wasan kwaikwayo dana dandamali.

Ya fara bayyana a cikin jerin wasanni mai suna 'Forest Uprising', sa'an nan kuma ya gabata a fim din sa na farko mai suna  'Fire in Winter' (A shekara ta Alif dari tara da tamanin da hudu). Ya nuna kwarewar sa na yin wasa a fim mai suna ‘The Bride’ (1990) bayan haka ya zama sanannen dan fim da kuma Jarumin kwaikwayon talabijan.

An zabeshi domin lambar yabon jarimin Jarumin kwaikwayo saboda matsayinsa a fim mai suna ‘A Faraway Place’  (a shekara ta dubu biyu da biyar) a bikin bajakolin fina-finan duniya na Crystal Simorgh na Fajr.

Ɗaya daga cikin ayyukansa mafi daraja shine wanda ya futo a matsayin Papa Roman Amun a cikin jerin wasan  ‘Prophet Joseph’ (a shekara ta dubu biyu da takwas) da kuma matsayin Abu-Moosa Ash’ari a cikin jerin wasan ‘Imam Ali’ (a shekara ta Alif dari tara da casa'in da bakwai zuwa takwas).

Matsayinsa na karshe a jerin wasan talabijin shi ne Amer bin-Masoud a cikin ‘The Rise of Mokhtar’ (a shekara ta dubu biyu da goma zuwa sha daya).

Amiri-Moqaddam ya rasu a wani hatsarin mota a shekara ta dubu biyu da goma sha daya.

1
Share