Atash Taqipour

 An haifi Taqipour, Atash a ranar hudu ga watan Afrilu a shekara da Alif dari tara da arba'in da biyar a garin Khoy. Taqipour yana da karatun dipiloma a fannen wallefe-wallafe kuma yayi karatu a fannin wasan kwaikwayo da shirye-shiryen wasanni a Jami'a.

Ya fara sana'ar sa na wasan kwaikwayo a shekara ta Alif dari tara da sittin da shida akan dandamali a wasa mai suna ‘The Reign of Zaman Khan’, wanda Roknoddin Khosravi ya shirya.

Wasu fina-finai da ya bayyana a cikin sun hada da ‘Under the Rain’ (a shekara ta Alif dari tara da tamanin da hudu), ‘The Bride of Halabja’ (a shekara ta Alif dari tara da casa'in), ‘The Passengers’ (a shekara ta Alif dari tara da casa'in da daya), ‘Pickpockets Don’t Go to Heaven’ (a shekara ta Alif dari tara da casa'in da daya), 'The Tenant ' (a shekara ta Alif dari tara da casa'in da biyu), 'The Moon and the Sun' (a shekara ta Alif dari tara da casa'in da biyar), 'Great Escape'  (a shekara ta Alif dari tara da casa'in da bakwai), 'Daybreak' (a shekara ta dubu biyu da biyar), ‘Under the Peach Tree’ (a shekara ta dubu biyu da biyar) da ‘Mother Tongue’ (a shekara ta dubu biyu da goma).

Ya futo a cikin jerin wasannin ‘Sarbedaran’ (1984), 'The Store' (1996), ‘The Tenth Night’ (a shekara ta dubu biyu da daya), ‘Loaded Gun’ (a shekara ta dubu biyu da biyu), 'A House in the Dark' (a shekara ta dubu biyu da uku), da 'Years of Snow and Violet' (a shekara ta dubu biyu da bakwai).

1
Share

Fina-finai da Jerin fina-finai

Dare Na Goma

Dare Na Goma

Imam Ali

Imam Ali