Ali-Asghar Hemmat

An haifi Hemmat, Ali-Asghar a ranar goma sha takwas ga watan Disamba shekara ta Alif dari tara da hamsin da biyu a garin Shiraz.  Ali-Asghar Hemmat Jarumin kwaikwayo ne kuma yana kyawata dandalin filin wasan talabijan, silima da sauran dandalin wasa. 

Yayi karatun sa a fannin dandalin wasan kwaikwayo sashen zane-zane na Jami'ar Tehran. A shekara ta dubu biyu da biyu ya sami damar karɓar takardar farko na zane-zane a fannin 'yan wasan kwaikwayo na kungiyar masu kimantar 'yan wasan kwaikwayo ta Iran.

Bayan futowa a matsayin sa na Jarumi, yana aikin kwaliyan 'yan wasa a fina-finai daban-daban.

Ya bayyana a cikin fina-finai da dama, ciki har da ‘Out of Range’ (a shekara ta Alif dari tara da tamanin da bakwai), ‘In the Storm's Path’ (a shekara ta Alif dari tara da tamanin da takwas), ‘The Havana Brief’ (a shekara ta dubu biyu da biyar), ‘A Sugar Cube’ (a shekara ta dubu biyu da tara) da kuma ‘Insomnia’ (a shekara ta dubu biyu da tara). Yana futowa a wasu shirye-shiryen talabijin irin su ‘Imam Ali’ (a shekara ta Alif dari tara da casa'in da shida), ‘The Friendship Agency’ (a shekara ta Alif dari tara da casa'in da takwas), ‘Like No One’ (a shekara ta dubu biyu da takwas), ‘Panacea’ (a shekara ta dubu biyu da goma sha uku) da ‘Puzzle’ (a shekara ta dubu biyu da goma sha hudu).

Yana auren Jarumar kwaikwayo mai suna Afsar Asadi.

11
Share

Fina-finai da Jerin fina-finai

Imam Ali

Imam Ali