Asha Mehrabi

An haifi Mehrabi, Asha a ranar hudu ga watan Nuwamba shekara ta Alif dari tara da saba’in da uku.

Mehrabi tana da digiri dinta na farko a fannin Fassara Turanci da kuma na biyu a fannin Harkokin Duniya. Ta bayyana a fina-finai irin su ‘A Window Facing the Yard’ (A shekara ta dubu biyu da takwas), ‘Habib’ (A shekara ta dubu biyu da goma), ‘Yalda Dead End’ (A shekara ta dubu biyu da goma sha uku) da ‘Reversion’ (A shekara ta dubu biyu da goma sha hudu).

Mehrabi ta taka rawar gani a jerin wasanni da dama, ciki har da ‘Ancient Land’ (A shekara ta dubu biyu da takwas), ‘Building No. 85’ (A shekara ta dubu biyu da tara) ‘The Gradual Death of a Dream’ (A shekara ta dubu biyu da takwas), ‘The Chef’ (A shekara ta dubu biyu da goma), ‘Special Guests’ (A shekara ta dubu biyu da goma sha biyu), da ‘The Line’ (A shekara ta dubu biyu da goma sha hudu).

Bayan aikin ta na wasan kwaikwayo, marubuciya ce, tana sarrafa muryoyi da kuma bada umarni wajen shirye-shiryen rediyo da nade-naden wasanni.

Asha Mehrabi 'yar tsohon Jarumin kwaikwayon Iran ce mai suna Esmaeel Mehrabi.

1
Share

Fina-finai da Jerin fina-finai

Habib

Habib

It's All There

It's All There