Behnaz Jafari

An haifi Jafari, Behnaz a shekara ta Alif dari tara da saba'in da hudu a garin Tehran.

Behnaz Jafari wata Jaruman kwaikwayo ce a gidan telebijin, gidan silima kuma tana wasan dandamali. mai wasan kwaikwayo. Tayi karatun ta a fannin nazarin wallafe-wallafe a Jami'ar Musulunci ta Azad.

A shekara ta Alif dari tara da casa'in da hudu, ta fara sana'atta ta zama Jaruma a inda ta futo a wani fim mai suna 'Blue Scarf'. Ta bayyana a wasu shirye-shiryen talabijin, ciki har da ‘The Rise of Mokhtar (Mokhtarnameh)’ (a shekara ta dubu biyu da takwas), ‘Scarlet Soil’ (a shekara ta dubu biyu), ‘Time of Rebellion’ (a shekara ta dubu biyu zuwa dubu biyu da daya) da ‘It's All There’ (a shekara ta dubu biyu da goma sha hudu).

Jafari ta taka rawar gani a fina-finai  masu suna  ‘Fire and Water’ (a shekara ta dubu biyu), ‘The Visitor of Rey’ (a shekara ta dubu biyu), ‘Kandelous Gardens’ (a shekara ta dubu biyu da hudu), ‘A Time for Love’ (a shekara ta dubu biyu da bakwai).

Muhimmiyar rawar da Jafari ta taka  a fim mai suna ‘A House on the Water’ (a shekara ta dubu biyu da daya) yasa taci lambar yabon Crystal Simorgh na jarumar Jaruman kwaikwayo a Fajr International Film Festival a sashi na 20.

Ta kara cin lambar yabon jaruma a Jaruman kwaikwayo  a matsayin da ta futo a fim mai suna ‘The President's Cell Phone’ (a shekara ta dubu biyu da goma sha daya) na Fajr International Film Festival a sashe na talatin.

1
Share

Fina-finai da Jerin fina-finai

It's All There

It's All There