Ali Nasiriyan

An haifi Nasiriyan, Ali a ranar 4 ga watan Fabrairu a shekara ta Alif dari tara da talatin da biyar a birnin Tehran.

Ali Nasiriyan ya fara harkar wasan kwaikwayo da fina-finai a shekara ta Alif dari tara da hamsin da biyu. Ya fara wasan gidan kallo na Sinima da fim din ‘The Cow/ Saniya’ a (A shekarar Alif dari tara da sittin da tara). Nasiriyan ya shiga harkar da kafar dama, har ya kai ga zama fitaccen jarumin da yayi suna a cikin jaruman Iran.

Ya fito a fina-finai da jerin wasanni da dama. Daga cikin jiga-jigan wasanninsa akwai fina-finai kamar su ‘Kamal-ol-Molk’ (a shekarar Alif dari tara da tamanin da uku), da ‘Mirza Nowruz's Shoes/ Takalmin Mirza Nowruz’ (a shekarar Alif dari tara da tamanin da biyar), da ‘Captain Khorshid/ Kyaftin Khorshid’  (a shekarar Alif dari tara da tamanin da shida), da ‘Scent of Joseph’s Shirt/ Kanshin Rigar Yusuf’ (a shekara ta Alif dari tara da casa'in da biyar), da ‘The Silent King/ Sarki mai Shiru-shiru’ (a shekara ta dubu biyu da uku), da 'Saturday Hunter/ Mafaraucin Ranar Asabar' (a shekara ta dubu biyu da goma sha daya), da kuma 'Iran Burger/ Burger ‘Yar Iran' (a shekara ta dubu biyu da goma sha hudu).

Hakana ya fito a jerin fina-finai kamar su 'Sarbedaran’ a (a shekarar Alif dari tara da tamanin da hudu), da ‘Hezar Dastan’ (a shekarar Alif dari tara da saba'in da tara zuwa shekarar Alif dari tara da tamanin da bakwai), da 'The Wolves/ Dila' (a shekarar Alif dari tara da tamanin da shida zuwa bakwai), da 'The Lost Paradise/ Rashin Aljanna' (a shekara ta Alif dari tara da casa'in da shida), da 'Neighbors/ Makwabta' (a shekara ta dubu biyu), da 'Lighter than Darkness' a (a shekara ta Alif dari tara da casa'in da tara zuwa shekara ta dubu biyu da biyu), da 'Floating in a Bubble/ Iyo A Kumfa' (shekara ta dubu biyu da shida), da ‘The Forbidden Fruit/ Haramtaccen Kayan Marmari’ (shekara ta dubu biyu da bakwai), da 'Sheikh Baha'ee/ Shehi Baha’ee'  (shekara ta dubu biyu da uku zuwa takwas), da 'Mankind's Land/ Filin Dan Adam' (shekara ta dubu biyu da tara), da kuma 'Sparrow's Dream/ Mafarki Sparrow' (shekara ta dubu biyu da goma sha biyu).

Ya ci kyautar rubuta wasan ‘Nightingale in Love/ Soyayyar Tsuntsun Tsadda’ a shekara ta Alif dari tara da hamsin da bakwai. A shekara ta shekara ta dubu biyu da biyu, an bawa Nasiriyan babbar lambar girma ta Iran ta “Iranian National Treasure” a fannin wasan kwaikwayo da fina-finai.

1
Share