Amin Tarokh

An haifi Tarokh, Amin goma sha daya ga watan Agusta, shekarar alif dubu daya da dari tara da hamsin da uku, a garin shiraz.

Tarokh ya kammala karatun digirin farko a jami'ar Tehran, tsagayar karatu na fannin wasan drama da fasaha, sannan yayi karatun digiri na biyu a fannin sanin al'adu.

Saboda kwarewarsa na shekarau da yawa, yana daya daga cikin wadanda sukayi suna da nasara a cikin jaruman wasannan fina finai na kasar Iran, wadanda sukayi gajerun fina finai, jerin dogayen finai finai da kuma wasanni da dama.

Sannan kuma ya kasance daya daga cikin alkalai masu sa ido wajen shirin bikin 'yan wasan finai na kasa wanda akayi da dama.

Shi  ya kirkiri taron bita na jaruman fina finai mai suna 'Independent Acting Workshop', makarantar koyon zama jarumin fin ta farko a Tehran a shekarar alif dubu daya da dari tara da casa'in da hudu sannan ya koyar da wasan drama na tsawon shekaru hudu a jami'ar Australia ta kudu.

A shekarar alif dubu daya da dari tara da casa'in da bakwai, yaci kyautar 'Crystal Simorgh' a bikin 'yan wasan fina fina na duniya na Fajr a matsayin jarumi mafi bada goyon baya a cikin shirin ‘The Moon and the Sun’ a shekarar alif dubu daya da dar tara da casa'in da biyar, sannan an zabeshi a matsayin jarumin dayafi kowa kwazo na 'Crystal Simorgh' ta dalilin wani fim mai suna ‘The Havana Brief’ a shekara ta dubu biyu da biyar.

Ya fito a cikin shirin gajerun fina finai kamar haka ‘The Death of Yazdgerd’ a shekarar alif dubu daya da dari tara da tamanin da biyu, ‘Little Bird of Happiness’ shekarar alif dubu daya da dari tara da tamanin da bakwai , ‘Mother’ shekarar alif dubu daya da dari tara da tamanin da takwas, ‘The Devoted’ shekarar alif dubu daya da dari tara da casa'in da daya, ‘Sheikh Mofid’ shekarar alif dubu daya da dari tara da casa'in da biyar, ‘Conspiracy’ shekarar alif dubu daya da dari tara da casa'in da biyar, ‘Seven Stones’ shekarar alif dubu daya da dari tara da casa'in da bakwai, ‘Rules of the Game’ shekarar alif dubu daya da dari tara da casa'in da bakwai, ‘Saghar’ shekarar alif dubu daya da dari tara da casa'in da bakwai, ‘Barefoot in Heaven’ shekara ta dubu biyu da biyar, 'The 25th Hour' shekara ta dubu biyu da shida, 'The Boss' shekara ta dubu biyu da shida, 'Extreme Cold' shekara ta dubu biyu da tara da kuma 'Red Garden' a shekara ta dubu biyu da tara.

Jerin dogayen fina finai da Tarokh ya fito a ciki kuma sukayi suna aka sansu, sune ‘Sarbedaran’ a shekarar alif dubu daya da dari tara da tamanin da biyar, ‘The Green Journey’ shekara ta dubu biyu, ‘Coma’ shekara ta dubu biyu da bakwai, ‘Injury’ shekara ta dubu biyu da goma, 'Milky Way' shekara ta dubu biyu da goma sha hudu, da kuma 'Look Back Sometimes' a shekara ta dubu biyu da goma sha biyar.

1
Share