Akbar Abdi

An haifi Abdi, Akbar a ranar Ashirin da shida ga watan Agusta, a shekara ta Alif dari tara da sittin a garin Tehran. Bayan ya gama karatunsa na sakandare a shekara ta Alif dari tara da tamanin ya fara wasan kwaikwayo kadan-kadan. 

A lokaci daya ya samu karbuwa wajen jama'a yayin daya futo a wasu jerin wasanni n talabijan masu tsayi kamar ‘Boro Bia Neighborhood’ (a shekara ta Alif dari tara da tamanin da biyu) da kuma ‘I’m Late for school Again’ (a shekara ta Alif dari tara da tamanin da shida).

Abdi ya futo a wasan "yan camama kamar ‘Major Mayhem’ (a shekara ta Alif dari tara da tamanin da hudu), ‘The Man Who Became a Mouse’ (a shekara ta Alif dari tara da tamanin da da biyar), ‘The Tenants’ (a shekara ta Alif dari tara da tamanin da shida), ‘The Grand Cinema’ (a shekara ta Alif dari tara da tamanin da takwas) da ‘O’ Iran’ (a shekara ta Alif dari tara da tamanin da tara). Jarumin ya bayyana a fina-finai da jerin wasanni masu tsayi fiye da dari da ashirin.

Ya bayyana a fina-finai irin su ‘Doll Thief’ (a shekara ta Alif dari tara da tamanin da tara), ‘Nassereddin Shah Film Actor’ (a shekara ta  Alif dari tara da casa'in da daya), ‘The Devoted’ (a shekara ta  Alif dari tara da casa'in da daya), ‘Angel Day’ (a shekara ta  Alif dari tara da casa'in da uku), ‘A Gift From India’ (a shekara ta  Alif dari tara da casa'in da hudu), ‘Mr. Lucky’ (a shekara ta  Alif dari tara da casa'in da hudu), ‘Snowman’ (a shekara ta  Alif dari tara da casa'in da hudu), ‘The Sunny Man’ (a shekara ta  Alif dari tara da casa'in da biyar), ‘The Loser’ (a shekara ta  Alif dari tara da casa'in da biyar), ‘Night of the Fox’ (a shekara ta  Alif dari tara da casa'in da shida), ‘The Eagle’s Eye’ (a shekara ta  Alif dari tara da casa'in da takwas), ‘The Victorious Warrior’ (a shekara ta  Alif dari tara da casa'in da takwas), ‘The Rich and the Poor’ (a shekara ta  Alif dari tara da casa'in da tara), ‘The Outcasts’ (a shekara ta dubu  biyu da shida), ‘Flying Crow’ (a shekara ta dubu  biyu da bakwai), ‘Checkmate’ (a shekara ta dubu  biyu da takwas), ‘The Outcast 2’ (a shekara ta dubu  biyu da takwas), ‘Heartbroken’ (a shekara ta dubu  biyu da takwas), ‘The Extremists’ (a shekara ta dubu  biyu da tara), ‘The First Condition’ (a shekara ta dubu  biyu da tara), ‘The Outcasts 3’ (a shekara ta dubu  biyu da goma), ‘The President’s Cell Phone’ (a shekara ta dubu  biyu da goma sha daya), ‘Stingy’ (a shekara ta dubu  biyu da goma sha daya), ‘The Wrong Story’ (a shekara ta dubu  biyu da goma sha biyu), ‘Scandal’ (a shekara ta dubu  biyu da goma sha biyu), ‘The Backstreets of Shemroon’ (a shekara ta dubu  biyu da goma sha biyu), ‘Kindergarten Operation’ (a shekara ta dubu  biyu da goma sha biyu), da kuma 'The Ascended' (a shekara ta dubu  biyu da goma sha hudu).

Abdi ya kara bayyana a jerin wasanni irin su ‘Hygiene Neighborhood’ (a shekara ta  Alif dari tara da tamanin da hudu), ‘Imam Ali’ (a shekara ta  Alif dari tara da casa'in da daya), ‘Night of the Fox’ (a shekara ta  Alif dari tara da casa'in da tara), ‘Godfather’ (a shekara ta  Alif dari tara da casa'in da tara), ‘As Simple As That’ (a shekara ta dubu  biyu), ‘Under the City Sky 3’ (a shekara ta dubu  biyu da biyu), ‘Lost Innocence’ (a shekara ta dubu  biyu da biyu), ‘In the Eye of the Storm’ (a shekara ta dubu  biyu da uku zuwa tara), ‘Era of Constitutional Revolution’ (a shekara ta dubu  biyu da tara), ‘Open Parenthesis’ (a shekara ta dubu  biyu da tara zuwa goma), ‘Wake Up’ (a shekara ta dubu  biyu da goma sha daya), ‘Passion to Fly’ (a shekara ta dubu  biyu da goma sha daya), ‘Relatively Bad Guys’ (a shekara ta dubu  biyu da goma sha uku) da kuma ‘The Ascended’(a shekara ta dubu  biyu da goma sha hudu).

Kwarewar sa ya bashi damar futowa  matsayi daban-daban, kamar yaro da kuma babba a fim mai suna ‘The Magical Journey’(a shekara ta  Alif dari tara da tamanin da shida) , ya futo a matsayin yaron dake da tabain hankali a fim mai suna ‘Mother’ (a shekara ta  Alif dari tara da tamanin da rara) kuma ya futo a matsayin mace da namiji a fim mai suna ‘Snowman’ (a shekara ta  Alif dari tara da casa'in da hudu).

Ya lashe lambar yabo mai yawa, musamman saboda bayyanarsa a 'Mother' (a shekara ta  Alif dari tara da tamanin da tara) da kuma ‘I’m Sleepy’ (a shekara ta dubu  biyu da goma sha biyu) don kyautar fitaccan jarimi a bikin bajakolin fina-finan duniya na Crystal Simorgh na Fajr.

1
Share