Akram Mohammadi

An haifi Akram a shekarar alif dubu daya da dari tara da hansin da takwas a garin Tehran na kasar Iran.

Akram tayi kwasa kwasai kadan na zama jarumar wasan fina finai, daga nan ta fara fitowa a jarumar wasan fina finai a shekara ta alif dubu daya da dari tara da tamanin da uku.

Bayan wannan, bada dadewaba, fitattar mai bada umurnin nan a harkar fim ta kasar Iran mai suna Ali Hatami ta bukaci Akram da shiga wani shirin fim dinta mai suna ‘Mother’ a shekarar alif dubu daya da dari tara da tamanin da tara, wanda a karshe yasa ta sami cancanta a zaben Crystal Simorgh a bikin bajakolin fina finai na kasa da kasa na Fajr.

Hakazalika Akram ta fito a shirin jerin fina finai masu tsawo na gidan talabijin wadanda suka hada da ‘The Patriarch’ a  shekarar alif dubu daya da dari tara da casa’in da uku zuwa shekarar alif dubu daya da dari tara da casa’in da biyar, ‘The Green House’ shekara ta alif dubu daya da dari tara da sittin da shida, ‘The Tenth Night’ shekara ta dubu biyu da daya, 'Lighter Than Darkness' shekarar alif dubu daya da dari tara da casa’in da tara zuwa shekara ta dubu biyu, 'The First Night of Peace' shekara ta dubu biyu dabiyar, 'Operation 125' shekara ta dubu biyu da takwas, 'Light and Shadow' shekara ta dubu biyu da goma sha daya, sai kuma 'Relatively Bad Guys' a shekara ta dubu biyu da goma sha uku.

Baya ga wadannan fina finan Akram ta fito a shirin fina finai da dama kamar su 'The Girl in the Sneakers' a shekarar alif dubu daya da dari tara da casa’in da takwas, 'Sam and Narges' shekara ta dubu biyu, 'Tambourine' shekara ta dubu biyu da takwas, sai fim dinta na karshe a shekarar dubu biyu da goma mai suna 'Men Are from Mars, Women Are from Venus'.

1
Share

Fina-finai da Jerin fina-finai

Dare Na Goma

Dare Na Goma

Passion To Fly

Passion To Fly