Afshin Hashemi

An haifi Hashemi, Afshin a ranar goma sha biyu ga watan Oktoba a shekarar Alif dari tara da saba’in da biyar a birnin Tehran.

Afshin Hashemi yana da digiri dinsa na farko a fannin masannin kimmiyar sinadirai na injiniya da kuma ta biyu a fannin darakta. Ya fara sana’arsa na zama dan wasan kwaikwayo a wasan dabe kuma a ka fara hasko shi a wasa mai suna ‘So Close, So Far’ a shekara ta dubu biyu da uku.

Wasu daga cikin fina-finan da ya taka rawa su ne ‘Barefoot in Heaven’ (a shekara ta dubu biyu da biyar), ‘In the Name of Father’ (a shekara ta dubu biyu da hudu), ‘The Child and The Angel’ (a shekara ta dubu biyu da takwas), ‘Please Do not Disturb’ (a shekara ta dubu biyu da tara).

Hashemi ya bayyana a jerin wasanni da dama, ciki har da ‘Bench’ (a shekara ta dubu biyu da biyar zuwa shida), ‘Saadat Guesthouse’ (a shekara ta dubu biyu da shida), ‘The Safe’ (a shekara ta dubu biyu da tara) da kuma ‘The First Choice’ (a shekara ta dubu biyu da goma sha uku).

Banda zama dan wasan kwaikwayo, ya shirya fim mai suna ‘I Hope You Are Not Tired’ (a shekara ta dubu biyu da goma sha biyu) kuma ya iya wasa da  wani kayan kidar gargajiya mai suna “Kamancheh”.

1
Share

Fina-finai da Jerin fina-finai

So Close, So Far Away

So Close, So Far Away