Aliram Nouraee

An haifi Nouraee, Aliram a ranar bakwai ga watan Afrilu a shekarar Alif dari tara da saba'in da bakwai a garin Tehran. Aliram Nouraee yana da takadar digiri dinsa a kimmiyan Kwamfuta. A shekara ta Alif dari tara da casa'in da bakwai ya fara sana'arsa na wasan kwaikwayo.

Nouraee ya koyi wasan kwaikwayo ne a lokacin daya shiga wata ƙungiyar wasan kwaikwayo na Jami'ar Jahad Daneshgahi. A wannan lokacin, ya yi wasanni da dama a fagen wasa na birnin Tehran da kuma bukukuwa daban-daban na wasan kwaikwayon dalibai.

Fim dinsa na farko da aka hasko shi mai suna ‘Dawn’ (a shekara ta dubu biyu da biyar) da kuma cikin jerin wasan talabijan mai suna ‘A Sunny Night’ (a shekara ta dubu biyu da daya) ya ba shi daraja sosai inda mutane suka so shi.

Nouraee ya bayyana a cikin jerin wasannin talabijan da yawa, ciki har da ‘Last Song of the Phoenix’ (a shekara ta dubu biyu da biyu), ‘Dirty Money’ (a shekara ta dubu biyu da uku), ‘Jaber Bin Hayyan’ (a shekara ta dubu biyu da shida), ‘Infiltration’ (a shekara ta dubu biyu da goma sha uku) da kuma ‘Matador’ (a shekara ta dubu biyu da goma sha uku).

An kara hasko shi a fina-finai daban-daban irin su ‘The Golden Collars’ (a shekara ta dubu biyu da goma sha daya), ‘The Eighth Day of The Week’ (a shekara ta dubu biyu da goma sha daya), ‘Reparation’ (a shekara ta dubu biyu da goma sha daya) da ‘Iran Orphanage’ (a shekara ta dubu biyu da goma sha hudu).

Bayan wasan kwaikwayo, yana koyar da wasan fada.

1
Share